Wannab hoton wasu fusatattun Matasa ne da ke farfasa wata motar soji a garin Jos na jihar Plateau ranar Juma'a da safe bayan barkewar tarzoma, sakamakon labarin kisan mutum 11 a gidansu a kan hanyar Rukuba.

Idan baku manta ba, mun kawo maku labarin yadda wasu yan bindiga suka kai farmaki a gidan wata fitacciyar mata mai suna Mama-Kogi a gidanta da ke kan hanyar Rukuba ranar Alhamis, suka yi mata kisar gilla tare da yayanta su 9 har da makwabta da wata mata mai juna biyu.

Tarzomar ta bazu daga Rukuba zuwa Gada-biyu inda aka kashe mutum 2 kuma aka kone chaji ofis na yansanda, hakazalika ana fargaban an kashe wani mutum a garin Akpata. Karin wurare da tarzomar ta rutsa da su har da mahadar Asibitin Ola, Katako da Randabawal na Polo, inda aka kone wata motar soji kirar Hilux.

Masu tarzomar sun yi zargin cewa duk da yake maharan sun kwashe kusan awa 4 suna ta'asa a wannan yankin, amma jami'an tsaro basu je ba domin su bayar da kariya ga al'ummar wannan wuri. Tuni dai hukumar yansanda na jihar Plateau ta sanya dokar hana fita daga Magariba zuwa Asuba.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Post a Comment

 
Top