Shugaban Majalisar Dattijai kuma shugaban kwamitin da jam’iyyar PDP ta nada a kan zaben Gwamnan da aka gudanar a jihar Osun, Dakta Abubakar Bukola Saraki, ya bayyana sakamakon zaben da aka sake gudanarwa a jihar Osun a matsayin zaben jeka na yi ka, kuma gaba dayan zaben abin takaici ne ga tsarin dimokradiyyarmu a wannan lokacin da muke ciki, ya kuma bukaci ‘yan jam’iyyar PDP a fadin jihar da su kasance masu bin doka da oda su kuma saurari matakin da jam’iyyar za ta dauka.

Wadannan bayanan sun fito ne a sanarwa da mai ba shi shawara na musamman a kan harkokin watsa labarai Mista Yusuph Olaniyonu, ya sanya wa hannu, ya kuma kara da cewa, Saraki ya ce, “a ranar Alhamis muka ga danniyya kirikiri ga zaben da mutanen jihar Osun suka yi a zaben zagaye na biyu da aka yi, an tafka magudi da barazana ga masu zabe tare da cin mutumcin masu zabe.
Masu sa ido na ciki da kasashen wajen sun fuskanci barazana a yayin da aka hanasu isa runfunar zabe, ‘yan banga da ‘yan ta’adda sun tafka ta’addaci, jami’an tsaro kuma na kallo sun kasa yin komai a kai.

“kamar yadda na fada kwanaki da suka wuce, wannan shiga zabe a zagaye na biyu an shiya shi ne don jam’iyya mai mulki ta aiwatar da magudin zaben da ta shirya ba tare da sanya ra’ayin jama’a a gaba. Irin wannan zaben abin takaici ne ga tsarin dimokradiyyarmu, hakan kuma yana sanya kokwanto a kan hukumomin da aka dorawa alhakin kare wannan dimokradiya ta mu, hakkin kare kuri’un ‘yan Nijeriya baki daya, kamar yadda suka nuna ta hanyar kuri’ar da suka jefa tun da farko.

Abin daya sa kena hukumar zabe INCE ta dauki fiye da awa 10 kafin ta iya tattara kuri’un da aka jefa a runfunan zabe 7 da ke da kuri’u 2000 kacal, lallai wannna a kwai alamun tambaya a ciki.

“Abin mamaki ne, a zaben da aka gudanar a ranar Asabar, ‘yan takarar jami’yyar PDP dana APC suna tafiya a matsayin kunne doki sai ga shi bayan kwana 4 kawai, bayan sun gudanar da harkokin magudin su, wai sai gashi dan takarar jam’iyyar APC ya kwashe dukan kuri’un da aka jefa tare da bai wa dan takararmu wasu ‘ya kwaranin kuri’a.
“Ya na da mahimimanci ‘yan Nijeriya da kuma ‘yan kasashen waje su tabbatar da ba a dawo da hannun agogo baya ba a kan nasasarorin da aka samu ta fannin zabe kamar yadda a aka yi a zaben da ya gabata na 2015.

Bai kamata mu mayar da harkar dimokradiyyar mu ya zama abin wasa ba, kamar yada a ka gudanar da zaben jihar Osun, zaben jihar Osun kamar manuniya ce ga yadda za a gudanar da zaben 2019, wannan yana nuna cewa, zaben ba zai zama a cikin adalci ba a dukkan kananan hukumomin kasar nan guda 774 a jihohi 36 na kasar nan, wannan abin takaici ne kwarai da gaske.

“Ina son yin kira ga ‘yan jam’iyyar APC da dan takarar kujerar gwamnan na jam’iyyarmu ta PDP, Sanata Adeleke da kuma sauran jama’ar jihar Osun din gaba daya das u sani cewa, lallai bayan wahala sai dadi, lallai mun yi kokarinmu ta hanyar sadaukarwa bayan aiki na watanni da dama, to kowa ya kwantar da hankalinsa mu tsayu a kan akidar jam’iyyarmu ba tare da gudu ko jada da baya ba, nasara na nan tare da mu ko mai dadewa.
Shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki yana gaisawa da jama’a a yayin da ziyarci tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, bayan da ya gana da shugabannin jam’iyyar PDP ta jihar jigawa, ranar Alhamis 27 ga watan Satumba 2018.

©Leadershipayau

Post a Comment

 
Top