Wani direba dake aiki a fadar shugaban kasa me suna Offre yayi yunkurin kashe kanshi ta hanyar rataya saboda tsananin rayuwa da kuma rashin kyawun Albashi.
Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa, mutumin na karbar albashin dubu 25 duk wata kuma yana da mata da 'ya'ya biyu, ma'aikatan fadar gwamnatin sun bayyana cewa an sami direban a dajin Kubwa dake babban birnin tarayya Abuja rataye a jikin bishiya ya rataye kanshi.
An gano cewa Offre na yunkurin kashe kanshine bayan da matarshi ta dawo gida ta tarar da sakon da ya bari na takarda da ya bayyana haka, ai kuwa bata yi wata-wata ba ta sanar da makwauta halin da ake ciki, nanne aka shiga nemanshi lungu-lungu inda aka tarar dashi sagale a jikin bishiya yana reto.
Mutane sunyi tsammanin ya mutu amma ana cikin tafiya dashi sai ya farka.
Da yake magana akan lamarin da ya faru yace aikin shedanne kuma bazai iya tuna yanda lamarin ya faru ba.
Babban sakataren fadar shugaban kasa, Jalal Arabi ya tabbatar da faruwar wannan lamari inda yace mutumin yayi nadamar abinda ya aikata kuma yayi alkawarin hakan ba zai sake faruwa ba.
Dangane da batun Albashin ma'ikacin kuwa, sakataren yace babu abinda zasu iyayi saboda tsarin gwamnatin tarayyane haka.
Post a Comment