Rahotanni daga babban filin wasa na Haliru Abdu da ke garin Birnin kebbi sun tabbatar mana cewa jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kebbi ta ba Gwamna Atiku Bagudu dama domin tsayawa a karkashin jam'iyyar don takarar kujerar Gwamnan jihar Kebbi a zabe na 2019.

Hakazalika majiyarmu ta tabbata mana cewa ba a gudanar da wani zaben fid da gwani ba tsakanin Gwamna mai mulki Atiku Bagudu, da wanda wasu jama'arsa daga kasar Zuru da Yauri ke dakon sauraron ko zai tsaya a wannan zabe wataau Alh. Ibrahim Mera Chiroman Kabbi.

Ku biyo mu domin karin bayani....


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Post a Comment

 
Top