Iskar juyin juya hali na ci gaba kadawa a Saudiyya,inda a karo farko a tarihin kasar,wata mace ta fara bada labarai a tashar talabiji.
A jiya ne wata mai bada labarai mai suna Wiyam Ad-Dahil ta bayyana gaban masu kallon tashar talabijin Saudi TV.
Bayan ta kammala bada manyan labarai,Dahil ta ci gaba da gabatar da jadawalin gudanar da shirye-shiryen tashar tare da abokin aikinta,Omar An-Neshwan.
Matashiyar ta yi karatu a tsangayar ilimin jarida a jami'ar hadakan Amurka da Lubnan,inda daga bisani ya yi aiki a gidan jaridar Al-Hayat wanda cibiyarsa ke a Landan da kuma tashoshin talabijin Al Jazeera da Al Arab na kasar Qatar.
Tun a lokacin da akalar mulkin masarautar Saudiyya ta kasance a hannun yarima mai jiran gado Muhammad ben Salman,aka bai wa mata izinin tuka mota,kafa kamfanoni,aiki a ma'aikatar shari'a,halartar gasannin motsa jiki,zuwa gidajen sinima da na kallon wasan kafa da dai sauran su..
Manufar saudiyya ita ce habbaka aikin matan kasar daga kashi 22 cikin dari zuwa 30 kafin shekarar 2030.
TRThausa.
Post a Comment