Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, gwamnatinsa ta himmatu wajen samun nasara a yakin da take yi da matsalar cin hanci da rashawa, yayin da mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya gargadi mahandama dukiyar kasar da su maido da kudaden sata ko kuma su fuskanci tuhuma.


Shugaba Buhari na magana ne a birnin New York a wani taron tattaunawar koli ta Kungiyar Kasashen Afrika mai taken “ Samun nasara akan cin hanci da rashawa ita ce kyakkyawar hanyar kawo sauyi a Afrika”.

Shugabannin Kasashen na Afrika sun amince wa Buhari da ya jagoranci yaki da cin hanci da rashawa a Afrika.

Shugaba Buhari ya ce, nahiyar Afrika na tafka asarar kimanin Dala biliyan 50 a kowacce shekara saboda hada-hadar haramtattun kudade a yankin.

A bangare guda, mukaddashin shugaban Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Najeriya Zagon Kasa, Ibrahim Magu, ya gargadi wadanda suka sace dukiya da kadaorin kasar da su mayar da su ko kuma su fuskanci tuhuma.

Mr. Magu da ke ganawa da manema labarai a birnin New York na Amurka ya bayyana cin hanci da rashawa a matsayin mugun abu da ba za su amince da shi ba.

Magu ya nanata cewa, za su cafke mahandaman dukiyar Najeriya komin dadewa.

@RIFHausa

Post a Comment

 
Top