Wani manomi a Kenya yana cikin mutane biyar da suka yi nasara a duk fadin duniya, da kamfanin Facebook ya ba kowannensu dala milyan daya.
An yi hakan ne ta hanyar Shirin Jagoranci na Al'ummomi. Noah Nasiali ya bude wani shafin facebook mai suna Africa Farmers' Club, wato kungiyar manoman Afirka.
Manomin dai shi ne dan asalin Afirka da ya yi nasara a ka zabe shi cikin jerin mutanen da su ka yi nasarar cin kyautar dala miliyan daya da facebook din ya ware.
Kungiyar da Noah ya kafa na taimakawa manoma a sassan Afirka da dama wajen yada ilimin dabarun noma daban-daban, wadanda su ka kai ga kara yawan albarkatun noma da riba. Baya ga Mista Mosiyali, akwai wasu karin 'yan Kenyar biyar da su ka shiga cikin jerin mutane sha hudu daga wasu kasashen Afirka da kowannensu zai samu dala dubu hamsin, kuma sun bude shafukan Facebook ne da ke kokarin magnace wasu matsaloli.
A cikin watan Oktoba ne Facebook din zai shirya wani gagarumin biki ga wadanda su ka yi nasara a Jihar Carlifornia da ke Amurka, kuma za taimaka musu da karin horo da kayan aiki don inganta ayyukan nasu a inatnet da ma zahiri.
mungode..
Post a Comment