Rahotanni daga Jos na jihar Plateau sun ce wasu 'yan bindiga sun kashe mutum 14 ranar Alhamis da dare a kan hanyar Rukubu. Wadanda aka kashe mutum tara ne a gida daya, yayin da aka kashe wsu mutum biyar.

Bayanai sun ce 'yan bindigar sun kai harin ga al'umma mazauna hanyar Rukubu wacce ta hade Barikin Rukubu da misalin karfe 8:00 na dare, kuma suka yi ta harbin mai uwa da wabi.


Wata majiya ta labarta cewa jama'a cikin rudani sun fara tserewa daga unguwar Kasuwar Terminus domin neman mafaka. Amma an ga Soji cikin shirin ko ta kwana sun ja daga a wasu muhimman sassa a garin domin bayar da kariya da tabbatar da lafiyar jama'a.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Post a Comment

 
Top