Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho ya bayyana cewa daga yanzu dan wasan kungiyar Paul Pogba bazai sake zama mataimakin kaftin din kungiyar ba saboda wani dalili.

Rahotanni sun bayyana cewa Mourinho ya shaidawa Pogba cewa bazai sake zama mataimakin kaftin kungiyar ba kuma a gaban ragowar ‘yan wasan kungiyar sakamakon wasu kalamai da dan wasan yayi bayan kungiyar ta buga wasa 1-1 da kungiyar Wolberhampton a satin daya gabata.
Sai dai Mourinho har yanzu bai bayyana dalilinsa na cire Poga daga zama mataimakin kaftin din kungiyara ba kuma ya karyata zancen da akeyi na cewa sun sake samun sabani da dan wasan a ‘yan kwanakin nan.

Mourinho ya tabbatar da cewa daga yanzu Pogba bazai sake saka kaftin din kungiyar ba bayan kungiyar ta tashi daga wasan da sukasha kasha a hannun kungiyar Derby County a wasan cin kofin Karabawo da aka fara bugawa a rabar Laraba
“Maganar gaskiya shine Pogba bazai sake zama kaftin din kungiyar nan ba saboda daman nine nace yazama mataimakin kaftin yanzu kuma na cireshi amma kuma babu wata rigima a tsakaninmu” in ji Mourinho
Yaci gaba da cewa “Mutumin dayace Pogba bazai sake zama kaftin din kungiyar ba shine tun da farko yace Pogba zai iya saka kaftin din kungiyar idan Balencia baya nan kuma ba kowa bane illa ni”
Pogba dai ya saka kaftin din kungiyar sau uku a wannan kakar kuma na kwana kwanan nan ma shine wanda yasaka a wasan da kungiyar tasamu nasara daci 3-0 a wasan zakarun turai da kungiyar Young Boys.

Post a Comment

 
Top