Rahotanni daga jihar Osun sun ce jami'an tsaro sun damke wasu matasa kuma suka tilasta su kwantawa a kasa bayan an yi zargin cewa an kama su da Guraye Da Layu tare da ababe da aka haramta zuwa da su a wajen kada kuri'a, yayin da shi kuma matashi guda daya ya gamu da fushin jami'an tsaro bayan sun ja shi a kasa suka banka masa barkonon tsohuwa, domin yana daukan hotuna daga wani gidan sama a garin Osogbo.

Hakazalika bayanai sun ce an sami 'yar hatsanini sakamakon wani rudani da ya kaure a Mazaba ta 17 Rumfa  ta 5, bayan da misalin karfe 11:50 na safe aka ji karar harbin bindiga daga bayan runfar da ake kada kuri'a, sakamakon haka masu kada kuri'a da yan jarida suka nemi mafaka domin ceton ransu, nan take yansanda suka mayar da martani da harbe harbe mai karfin gaske a cikin iska.

Amma komi ya koma daidai kuma jama'a sun ci gaba da kada kuri'arsu .

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Post a Comment

 
Top