An gano wasu takardun da shahararren masanin fasaha na kasar Burtaniya,Isaac Newton ya rubuta a karni na 17 miladiyya,inda ya ce a shekarar 2060,Annabi Issa zai dawo duniya sannan za a yi tashin kiyama.


An tabbatar da cewa,masanin wanda ya zo duniya a shekarar 1643 ya yi fice haikan wajen zurfafa bincike kan tsarkakkun litattafai.

A takardun da aka gano Newton ya ce: "Tabbas za a yi tashin duniya a shekarar 2060.Amma har yanzu na kasa gano musababbin hakan".

Marubuci Florian Freistetter ya bada cikakken bayanin wannan hasashen na busa kaho da Newton ya yi a littafinsa mai suna: "The Asshole Who Reinvented the Universe",inda ya ce ga dukkan alamu yakin addini,annoba ko kuma wani babban bala'i ne zai rutsa da wannan duniyar.
TRThausa.
30 Sep 2018

Post a Comment

Emoticon
:) :)) ;(( :-) =)) ;( ;-( :d :-d @-) :p :o :>) (o) [-( :-? (p) :-s (m) 8-) :-t :-b b-( :-# =p~ $-) (b) (f) x-) (k) (h) (c) cheer
Click to see the code!
To insert emoticon you must added at least one space before the code.

 
Top