Assalamu Alaikum Malam Wani bawan Allah ne ya Auri kanwata, sai daga baya muka gane ya ha’incemu sakamakon rashin mazantaka da baya da shi, daga baya da asirinsa ya tonu sai ya saketa, shin malam za tayi Idda ne? Don babu wata mu’amalar Aure da ya taba shiga tsakaninsu? Wa’alaikum assalam, Mutukar ba su taba kwanciyar aure ba, ai babu idda akanta, kamar yadda aya ta: 49 a suratul ahzaab take nuni zuwa hakan.
Mungode.
Post a Comment