isyaku.com | 25-9-2018 |

Hotunan wasu takardu da muka samu daga garin Yauri na jihar Kebbi, sun nuna cewa Kansiloli goma na karamar hukumar sun saka hannu a wata takarda da ke nuna cewa sun tsige shugaban karamar hukumar Yauri a ranar 25 ga watan Satumba 2018.

Kansilolin sun rubuta cewa shugaban Karamar hukumar Yauri ya kasa gabatar da kansa a wani komiti da aka kafa domin ya kare kanshi bisa zargi da ake yi masa, amma daga bisani wani hadiminsa ya zo yace masu suna da aiki a gabansu daga bisani ya tafi abinsa.

Takardar ta ce, sakamkon haka ne Kansilolin da suka zayyana sunayensu a takardar suka tsige shugaban karamar hukumar duk da yake ba inda aka ambaci sunans shugaban karamar hukumar ta Yauri a cikin takardar.

Hakazalika takardar ta ce ofishin shugaban karamar hukumar na nan a rufe kuma jami'an tsaro suna bayar da tsaro a wajen.

Yunkurin mu na jin ta bakin kakakin hukumar yansanda na jihar Kebbi ya ci tura, domin dai bai mayar da martani a sakon SMS da muka tura masa ba, hakazalika bai amsa kiraye-kirayen wayar Salula da muka yi masa ba kafin lokacin rubuta wannan rahotu.

A bangaren shugaban karamar hukumar ta Yauri da jagoran Kansiloli da suka ce sun tsige shugaban karamar hukumar , su ma bamu same su ba a wayar Salula domin tantance lamarin.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Post a Comment

 
Top