Rahotanni daga kasar sipaniya sun bayyana cewa tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Raul Gonzales yana dab da kammala karatunsa domin zama mai koyar da yan wasa a wata mai kamawa idan lokacin karatun nasa ya kare.
Rahoton yace nan gaba kadan idan ya karbi shaidar kammala karatun nasa zai fara aikin koyar da yar karamar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid wato (Castilla) inda tuni aka fara shirye shiryen bashi kungiyar.

Raul dai yakoma Real Madrid bayan wasu shekaru daya shafe a kasar Saudiya yadawo kungiyar ne a matsayin mai bada shawara kuma tuni yafara koyar yadda zai koyar da ‘yan wasan na Real Madrid.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai tayi garambawul a wasu daga cikin masu horar da yan wasanta a matakin matasan yan wasa kuma tuni aka saka Raul a lissafi yayinda shima tsohon dan wasan kungiyar, Guti, aka bashi wata karamar kungiya domin shima yafara koyar da ita amma idan bai samu wata kungiya ba a gasar laliga a shekara mai zuwa.

Guti dai tuni ya kammala karatunsa na koyarwa kuma ya taba koyar da wata karamar kungiya a kasar ta sipaniya a shekarar data gabata sannan kuma an taba saka sunansa a matsayin wadanda zasu iya maye gurbin Zidane kafin kungiyar ta dauki sabon mai koyarwa
Raul ya zura kwallaye 307 a Real Madrid cikin shekaru 15 da yayi a kungiyar sannan kuma ya lashe manyan kofu a 16 ciki har da gasar laliga guda shida da gasar zakarun turai guda uku.

Post a Comment

 
Top