Mawaki Ado Gwanja zai angwance - Zai auri masoyiyar sa Maimuna - A 13 ga watan Oktoba za'a daura auren Fitaccen jarumin nan da kan fito a fina-finan Hausa na masana'antar Kanyywood kuma mawaki da tauraruwar sa ke haskawa a wannan zamanin, Adamu Isa wanda aka fi sani da Gwanja ya shirya tsaf domin zama ango a ranar 13 ga watan da ya gabata na Oktoba.



  Kamar yadda muka samu, mawakin Ado Gwanja dai zai auri masoyiyar sa ce mai suna Maimuna Kabir Hassan kuma ana sa ran daura auren ne a garin Kano a ranar ta 13 ga watan gobe da misalin karfe 11 na safe a kan titin zuwa gidan Zoo.

 Ado Gwanja yanzu yafi shahara ne a harkokin wakokin bukukuwa da wadanda suka shafi mata duk kuwa da cewa a wasu lokuttan yakan yi wakokin fina-finai da kuma na siyasa. Haka zalika mun samu cewa a cikin wata fira da mawakin yayi da majiyar mu a kwanan baya, Ado Gwanja ya bayyana cewa dalilin da ya sa yafi karkata wajen yiwa mata waka shine domin sune ke yin ruwa da tsaki a harkar bukukuwa. A wani labarin kuma, Jarumar nan ta masana’antar Kannywood wadda ta shahara wajen fitowa a matsayin uwa a fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood da dama watau Hadizan Saima ta bayyana dalilin ta da ya sa ya zuwa yanzu bata marmarin sake yin aure kwata-kwata.

Fitacciyyar jarumar wadda ta ce ta shafe akalla sama da shekaru ashirin a gidan miji ta ce ita yanzu kam sai dai ta aurar da nata 'ya'yan amma ita ta ci girma don kuwa an sha ta ta warke inda game da maganar ta aure ce.

©naijhausa.com

Post a Comment

 
Top