Hukumar sojin Najeriya ta gano motar Janar (mai ritaya) a karkashin wani kududdufi dake unguwar Dura Du a karamar hukumar Jos ta kudu, bayan fiye da sati uku ana nemansa. Manjo Janar Idris Alkali ya bace ne tun ranar 3 ga watan Satumba a hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja.

 Rahotannin da hukumar soji ta tattara sun gano cewar Alkali ya bata ne a karamar hukumar Jos ta kudu. Babu tabbacin ko gawar Alkali na cikin motar. Sai dai Birgediya Janar Umar Mohammed, shugaban rundunar soji dake farautar neman inda Janar din yake, ya bayyana cewar zasu kwashe ruwan domin tabbatar da gawar Alkali na ciki ko akasin haka.

Tun a ranar 20 ga wata ne, Birgediya Janar Umar Mohammed, shugaban tawagar masu neman Janar Alkali, ya shaidawa gidan talabijin na Channels a yau, Alhamis, cewar sun tura rundunar soji zuwa yankin Dura Du dake karamar hukumar Jos ta kudu a jihar Filato.A cewar Mohammed, bayanai na bayan-bayan nan da suka samu sun tabbatar masu da ganin motar janar Alkali daf da wani tafki a yankin.

 “Mun zo nan ne bayan samun sahihan bayanai. Mun samu kusan tsawon sati guda muna nan, neman jami’in soja, Manjo Janar M. Alkali (mai ritaya), da har yanzu ba a san inda yake ba,” a cewar Mohammed. Birgediya Janar Umar Mohammed, shugaban tawagar masu neman Janar Alkali, ya shaidawa gidan talabijin na Channels a yau, Alhamis, cewar sun tura rundunar soji zuwa yankin Dura Du dake karamar hukumar Jos ta kudu a jihar Filato.

A cewar Mohammed, bayanai na bayan-bayan nan da suka samu sun tabbatar masu da ganin motar janar Alkali daf da wani tafki a yankin. “Mun zo nan ne bayan samun sahihan bayanai. Mun samu kusan tsawon sati guda muna nan, neman jami’in soja, Manjo Janar M. Alkali (mai ritaya), da har yanzu ba a san inda yake ba,” a cewar Mohammed. “Mun zo har inda tafkin rowan yake domin ganin ko zamu samu wani abu da zai kai mu ga gano inda Janar Alkali yake.

Wasu bayanai da muka samu sun bayyana cewar an tura wasu motoci cikin tafkin rowan. Rowan yana da zurfi sosai saboda wuri ne da ake hakar ma’adanai. Yanzu haka mun yanke shawarar yashe ruwan tafkin domin samun dammar ganin abinda ke can kasa,” kamar yadda Mohammed ya fada. Janar Alkali ya bata ne ranar 3 ga watan Satumba bayan ya bar Abuja zuwa Bauchi cikin wata bakar mota kirar Toyoto Corolla. Duk kokarin samun shi ya ci tura saboda wayar sa a kashe take.
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Hausa.naija.ng

Post a Comment

 
Top