— Allah madaukakin sarki yana cewa: "Da yini mai sheda, da yinin da ake halarta a cikinsa" (Suratul-Buruj: 3), A karkashin wannan aya abu huraira yana cewa: "Al-Yamul-Mau'ud: Ranar Al-kiyama, Wash-Shaheed: Ranar Juma'a, Wal-Mash-Huud: Ranar Arfa"

— Ibn Hibbana ya fitar da hadisi mai lamba (2759), da Imamu Ahmad (457/2), Hadisin Abu-Huraira Yardar Allah ta kara tabbata a gare shi: yake cewa Manzon Allah SAW yana cewa: "Babu wata rana mafi Al-khairi da rana ke fitowa, kuma ta fadi a cikin ta, bayan ranar juma'a".

— Imamun nasa'i ya fitar da hadisi mai lamba ta (1317), Daga Jabir Dan Abdullah yardar Allah ta kara tabbata a gare shi, yace Manzon Allah SAW yace: "Ranar Juma'a Sa'o'i goma sha biyu, daga cikinsu akwai wata sa'a, wacce bazaka samu wani bawa musulmi ba yana rokon Allah wani abu, face ya bashi, Ku nemeta karshen lokaci bayan sallal la'asar".

— Haka kuma Hadisin Umar Bn Khaddab Allah ya kara yarda dashi. Wanda Imamu Muslim ya fitar da hadisin mai lamba (3017), Imamul Bukhari (45), Imamun nasa'i (114/8), Turmizi (3043), (Ammar dan Abi Ammar yace: wata rana ibn abbas ya karanta aya ta ukku a cikin suratul m'ida gaban wani bayahude, sai baya huden yace: da mune aka saukarma wannan ayar da mun riki ranar da aka saukar da ita idi, sai ibn abbas yace: Ni nasan lokacin da aka saukar da wannan ayar, an saukar da ita aranar arfa, kuma ranar juma'a.) 

[Albani yace hadisin Hasan ne,] [Imamut turmizi kuma yace, hasan ne garibi, ta hanyar ibn abbas amma saheehi ne].

Allah ka sadamu da al-khairin wannan rana Ameen.

Post a Comment

 
Top