Vanguard ta ruwaito Rahama Sadau lokacin da ake tamyarta me tayi ko kuma me take tunin ya kamata ayi na ilmantar da yara mata da kuma hana yi musu auren wuri a Arewacin Najeriya?.
Rahama tace, wasu daga cikinsu suna yaki da maganar yiwa yara mata auren wuri da kuma karantar dasu duk da cewa maganace me sarkakkiya saboda da an tabo maganar auren wuri to addini zai shigo ciki.
Tace a nata bangaren tana zama da iyayen yara tana wayar musu da kai, kuma itama kadan ya hana a mata auren wuri tun tana 'yar shwkaru 13 da haihuwa.
Tace abubuwa da yawa sun faru amma suna iya bakin kokarinsu.
Da aka tambyeta ta yaya ta tsallakewa maganar yi mata auren a wancan lokaci?, sai tace a koda yaushe tana godewa mahaifiyarta saboda tana so su cimma burin rayuwarsu.
Post a Comment
Click to see the code!
To insert emoticon you must added at least one space before the code.