Jama’a barkanku da kasancewa da shafin arewamobile.com a wannan lokaci. Shafin da ya karkata wajen kawo maku bayanai kan abubuwan da suka shafi labaran kimiyya da nishadantarwa.

A yau kuma a yanzu cikin ikon Allah da yardar shi zan fayyace maku yanda zaku kwashi garabasar data ta browsing mai yawa a layukan wayoyin ku.
Wannan garabasa wacce takai 10GB ana samunta ne a layin Glo. A haka kenan masu amfani da layin Glo ne zasu iya morar wannan garabasa.

Yadda zaka more wannan garabasar

Da farko ya kasance kana da layin Glo, sai ka danna *603# don komawa tsarin Glo Jollification.

Daga nan sai kawai ka sanya katin dari biyu (N200) ta hanyar sanya kati ta banki ko kuma ta One card. Da zarar ka sanya N200 zaka ga sun baka bonus din 10.4GB.
Haka zalika in ka sanya katin naira dari(N100) ta bank ko kuma ta one card, to zasu baka rabin(½) waccen garabasar, ma’ana zasu baka 5.2GB.
Domin duna ragowar data dake cikin layin naka sai ka danna *122#.

Sources:arewamobile.com

Post a Comment

 
Top