Wani matashi da ake zargi dan kungiyar asiri ne ya gamu da fushin wasu matasa a Opolo da ke birnin Yenagoa a jihar Bayelsa, ana tuhumar wannan matashi da yi ma jama'a fashi da makami, har ma yakan halaka bayin Allah da basu ji basu gani ba a wannan yanki wanda kee kewaye da Rafi.


Majiyarmu ta ce wasu matasa ne da suka gaji da halinsa, suka yi gangami suka farauto shi a maboyarsa, suka zo da shi a cikin Kwalekwale daga inda yake boye suka dawo da shi a cikin garin Opolo, kuma suka yi masa dan karen duka.

Bayanai sun ce isowarsa ke da wuya a cikin Kwalekwale sai matasa da suka harzuka suka bi shi da duka da sara da adduna da bulala da sauran makamai domin ya zama izna ga sauran masu hali irin nashi. Ko a mako da ya gabata, matasa sun kashe wasu samari da aka zarge su da kasancewa yan fashi da makami kuma aka kone gawarsu a wannan garin na Opolo  da ya yi kaurin suna wajen  yawan  aikata fashi da makami da ta'addanci irin na yan kungiyar asiri.

Kalli bidiyo a kasa:



Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Post a Comment

 
Top