Rahotanni sun bayyana cewa abu ne mai wahala dan wasan Real Madrid, Marcelo, ya buga wasan da kungiyar za ta buga na hamayya da kungiyar Atletico Madrid a ranar Asabar sakamakon ciwo da dan wasan ya ji a cinyarsa.
Marcelo dai ya fita daga filin wasan ne a daidai minti na 72 da fara wasan da Real Madrid tasha kashi a hannun Sebilla da ci 3-0, duk da cewa babu wanda ya doke shi a lokacin da aka hangoshi yana dingishi da kafarsa.

“Ya samu matsala ne a cinyarsa saboda haka za mu jira muga abinda likitoci za su yi akai, kuma muna fatan ciwon nasa ba zai dauki lokaci mai tsawo ba, saboda dan wasa ne mai matukar amfani a wajenmu” in ji mai koyar da ‘yan wasan Real Madrid.

Sannan kuma an yi wa dan wasa Isco aiki, hakan ya sa bai mu buga wasan da suka sha kashi ba a hannun Sebilla, yanzu mai koyar da kungiyar yana da babban aiki a gabansa na sanin yadda zai yi ya samu nasara akan kungiyar Atletico ranar Asabar.
Shi ma dan wasa Jimenez na Atletico Madrid ya samu ciwo a wasan da kungiyar ta samu nasara akan sababbin hawowa, Huesca da ci 3-0, sai dai mai koyar da kungiyar, Diego Simeone ya ce, yana fatan dan wasan zai warke kafin ranar Asabar.
Sakamakon rashin Marcelo, ana ganin dan wasa Nacho ne zai maye gurbinsa duk da cewa ya fi kokari a tsakiyar baya, ko kuma a bangaren daman a baya, amma duk da haka dole da shi mai koyarwar zai yi amfani domin buga wasa kafin Marcelo ya warke.

Post a Comment

 
Top