A yau, asabar, ne wata kungiya mai cin gashin kanta (Global Integrity Crusade Network (GICN)) tam aka gwamnan jihar Adamawa, Muhammad Jibrilla Bindow, a kotu bisa zarginsa da yin cogen takardar makarantar sakandire, WAEC.


A takardar karar da jaridar TheCable ta gani, GICN ta nemi kotun tarayya dake Abuja ta tilastawa gwamna Bindow neman yin takara a zaben shekarar 2019 bisa dogaro da sashe 177 (d) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.

Ita dai kungiyar GICN na zargin gwamnan da gabatar da takardar kamala karatun sakandire ta karya, wanda yah aka laifi ne da kan iya raba mutum da mukaminsa ko a haramta masa yin takara gaba daya, idan an gano kafin zabe.

Kungiyar GICN na bukatar kotun ta sanar da hukumar jarrabawa ta kasashen Afrika na yamma (WAEC) da kuma hukumar zabe mai zamna kanta (INEC) da jam’iyyar APC da kuma hukumar ‘yan sanda maganar cogen takardar kamala sakandire da gwamnan ya yi domin su dauki matakin da ya dace.

Ko a kwanakin baya saida irin badakala tayi gaba da kujerar ministar kudi, Kemi Adeosun, bayan dogon lokaci ana ta kwarmato a kan cewar ta gabatar da takardar bautar kasa (NYSC) ta bogi domin a tantance ta a matsayin minista.
Naija.ng.

Post a Comment

 
Top