Hoton dauki da kanka ko kuma wanda ake kira da selfie a turance ya zama ruwan dare a wannan zamani inda kusan kowa na yi, saidai a baya an ruwaito yanda daukar irin wannan hoto ya kai wasu ga samun mummunan rauni ko rasa rayuwa, duk da dai hakan be cika faruwa ba.


A wannan karin ma wata matace a kasar Amurka da taje wani gidan shakatawa na birnin Michigan inda garin daukar hoton Selfie din a kusa da wannan dutsen da ake ganin hotonshi a sama, ta kauce ta fada cikin ruwan ta mutu.

Ma'aikatan gidan shakatawar sun bayyanawa manema labarai cewa wanine da yaga lokacin da matar ta fada ruwan ya dauko gawarta zuwa gabar ruwan kamar yanda fox news ya ruwaito.

Post a Comment

 
Top