Yanzu dai ana shirin yin zaben fitar da gwani a Jam’iyyar APC inda za a tsaida ‘Yan takaran da za su rikewa Jam’iyyar tuta a zaben da za ayi a 2019. A Ranar Lahadi ne dai ake sa rai za a tsaida masu neman takarar Gwamna.


Mun kawo jerin wasu Gwamnonin da sai sun dage wajen samun tikitin Jam'iyyar APC:

1. Gwamna Akinwumi Ambode

Yanzu haka Gwamnan Jihar Legas Akinwumi Ambode yana cikin wadanda za su gamu da cikas a wajen samun tikitin Jam’iyyar. Ambode zai kara da Babajide Sanwo-Olu da kuma Dr. Kadri Obademi Hamzat wadanda su ke tare da kusoshin APC.

2. Gwamna Umaru Jibrilla Bindow

Gwamnan Adamawa Jibrilla Bindow yana cikin wadanda sai yayi da gaske wajen samun tikitin APC a zaben fitar da gwani da za ayi. Bindow zai fafata da Surukin Shugaba Buhari wanda ke tare da Nuhu Ribadu da sauran manyan APC a Jihar Adamawa.

3. Gwamna Mohammed Abubakar

Wani Gwamnan da kujerar sa ke rawa shi ne Mohammed Abubakar na Jihar Bauchi. Yanzu dai APC ta ba sauran masu neman kujerar Gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar mai mulki irin su Dr. Mohammed Pate su kara da Gwamnan da yake kan kujera.

Dazu kun ji cewa Jam’iyyar APC ta canza ranar da za a tsaida Gwamnonin Jihohi. Yanzu za ayi zaben ne a Ranar 30 ga watan nan a maimakon Ranar 29 da aka tsara a baya inji Yekina Nebena.
Naija.ng.

Post a Comment

 
Top