Ronaldo wanda a yanzu haka yake kasar Brazil yana hutawa bayan yayi ritaya daga buga kwallo ya bayyana cewa ba a kowacce kungiya ake iya samun ‘yan wasa kamar Coutinho ba.
‘Barcelona tayi babban tunanin lokacin da tayi kokarin siyan dan wasa Coutinho saboda matashin dan wasa ne wanda yasan abinda yakeyi kuma yake da tunani sama dana wasu ‘yan wasan” in ji Ronaldinho
Yaci gaba da cewa ‘babban abin takaici a aduniya shine banyi wasa tare dashi a kungiya daya ba ko a Barcelona balle a Brazil kuma ina bakin ciki da wannan abu amma har yanzu ban fitar darai da buga wasa dashi ba anan gaba”
Ronaldinho ya dai shafe shekaru 5 a Barcelona bayan da ya rattaba kwantiragi a shekara ta 2003, ya lashe gasar Laliga har sau biyu da Spanish Super Cup da kuma gasar cin kofin zakarun turai.
Post a Comment
Click to see the code!
To insert emoticon you must added at least one space before the code.