Wasu Gwamnonin jam'iyar APC sun fara murna a cikin gidan Gwamnatin jihar Osun sakamkon rinjayen kuri'u da suka samu a kananan hukumomi 3 cikin hudu da aka sake gudanar da zabe a ranar Alhamis. Gboyega Oyetola na jam'iyyar APC ne ke kan gaba.

Oyetola ya lashe mazabu biyu a Ile-Ife ta kudu da kuri'u 283 yayinda Ademola Adeleke na PDP yana da kuri'u 15, A Ife ta gabas kuwa APC tana da kuri'u 126 yayin da PDP ke da kuri'u 2 kacal.

A dukannin mazabun, an lura babu ajent na PDP ko daya. Sai dai sakamakon kuri'u na Mazaba ta 5 runfa na  7 a Alekuwodu da ke Osogbo APC tana da kuri'u 299 yayin da PDP ta sami kuri'u 165.


Zababben Gwamnan jihar Ekiti Dr. Kayode Fayemi, Gwamnonin jihar Kano, Jigawa sun taya Gwamna Rauf Adesoji Aredbosala murnar nassarar Gboyega Oyetola.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Post a Comment

 
Top