Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Roman Abromobic, dan kasar Rasha, ya saka kungiyar a kasuwa ga duk wanda yakeson siyan kungiyar akan kudi fam biliyan uku.

A kwanakin baya dai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta fito ta karyata batun cewa an saka kungiyar a kasuwa saboda wasu dalilai amma kawo yanzu kuma bayanan da suke fitowa suna tabbatar da cewa akwai alamun gaskiya.

Wani rahoto da aka fitar a kwanakin baya ya nuna cewa Abromobic yanason siyar da kungiyar ne sakamakon rashin samun takardar shiga kasar Ingila dayake yawan samu daga hukumomin kasar.

A kwanakin baya wani shahararren attajiri dan kasar Birtaniya ya taya kungiyar fam biliyan biyu sai dai abune mai wahala Abromobic ya yarda ya siyar da kungiyar a wannan tayin duk da kungiyar ta kai shekara 15 a hannun sa.

Abromobic, mai shekara 59 yasamu matsalar sabunta biza ne daga hukumomin Ingila sakamakon danbarwar siyasar da take tsakanin kasashen Ingila da Rasha wadda tayi tsami a ‘yan watannin baya.

Tun bayan daya karbi ragamar tafiyar da kungiyar Chelsea, Abromobic ya lashe kofin firimiya guda uku da kungiyar sannan ya lashe kofin Europa dana zakarun turai sannan kuma kungiyar ta kai matsayin daya daga cikin manyan kungiyoyin da suke nahiyar turai ake maganarsu.

Post a Comment

 
Top