Da farko ina mai cike da alhinin kisan sojojin kasata Najeriya a garin Metele dake jihar Borno. Ina kuma bakin cikin yadda na ga wasu na siyasantar da lamarin saboda wani ya ci zabe ko wani ya fadi.
Dan jarida Ahmad Salkida da ya san ciki da wajen Boko Haram ya tabbatar da cewa wannan mummunan harin da yayi sanadiyyar asarar rayukan sojoji kusan 100 daga kungiyar ISIS ne ba Boko Haram ba.
ISWAP tayi Ikirarin kai harin wacce kuma ita ce reshen ISIS mafi hadari a duniya. Wacce a yanzu matasan Najeriya da kasashe rainon Faransa suke ta tururuwar shiga.
Yanayin yadda ake gudanar da Tsaron harkokin iyakokin Najeriya abin sosa zuciya ne. Mutane da dama na amfana da zubar da jinin mu da ake yi a Najeriya. Sun zuba jari mai karfi suna kuma kasuwanci da rayukan mu.
Yaki ne mai matukar sarkakkiya da ya ke bukatar Tuntubar mutane Daban-daban a Fannoni Daban-daban. Jami'an tsaron sirri, sojoji da 'yansanda kadai yakin ya fi karfin su.
Muna bukatar kishin kasa, dagewa da Addu'a da kuma zaben SHUGABA NAGARI.
Ina kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da a marsayinsa na tsohon Soja, a karrama sojojin da suka rasa rayuwar su. A mutunta iyalansu. A kula sosai da wadanda suka raunata. A kuma yi Addu'a ta musamman domin neman tsarin Allah akan wannan mummunan al'amari.
Post a Comment