Daren MAULIDI Yafi KOWANNE DARE DARAJA (HARDA DAREN LAILATUL QADRI)
  Wannan tattaunawa ce da ta gudana tsakanin SHEIKH YUSUF SAMBO RIGACIKUN (malamin SUNNAH/IZALA)
   Dakuma sheikh dahiru usman bauchi (malamin dariqa/tijjaniyya) ::::::::::

 Shkh Rigacikun:MALLAM naji wata magana da ban fahimceta ba Amma ance Kaine ka fadeta.
  Shkh dahiru:wacce magana ce?
Shkh rigacikun:Naji ance Kace Wai daren maulud yafi daren lailatul qadri.
  Shkh dahiru:kwarai kuwa aikaima idan nagaya maka dalilin nawa zaka yarda da hakan.
Shkh rigacikun:to malam Ina sauraronka.
  Shkh dahiru:ai daren lailatul qadri yanada daraja ne saboda ansaukarda alqur'ani acikinsa, shikuma daren maulud shine aka haifi annabi Muhammad (saw), kuma annabin yafi alqur'ani daraja.
----------
Shkh rigacikun:to ai MALLAM shi daren lailatul qadri Allah ne dakansa yafifita shi akan kowanne har fiyeda darare dubu talatin, shikuma maganar daren maulud QIYASI ne kayi dakanka kawai kature nassin ayar alqur'ani, kuma hakan kuskure ne awajen malaman ilmin addini.
------
Shkh dahiru:hmmm aidama nasan wancan nassin alqur'ani ne shikuma wannan qiyasi ne, kuma daman nasan ku yan izala nasan bazaku yarda ba (ku dole saidai abi nassi) Amma mudai haka zamuyi
------------------------mai karatu bari nakyaleku haka hirar tanada tsawo, ku masuyin mauludi kuji tsoron Allah karku bari arabaku da alqur'ani akaiku kintace da dabaru.
ALLAH yakara mana shiriya
ALLAH YAKEBO BAYINSA
                Amen.

Post a Comment

 
Top