Da yawa daga cikin masoya kwallon kafa ba su san ’yan kwallon da suka fi samun jan kati a lokacin da suka yi kwallon kafa ba. A yayin da wasu daga cikin ’yan kwallon tuni suka yi ritaya wasu kuwa har yanzu ana damawa da su a wasan kwallon kafa duk da shekaru sun yi musu nisa. Aminiya ta yi nasarar lalubo bayanan wadannan ’yan wasa da kuma yawan jan katin da kowannensu ya samu:
1. Gerardo Alberto Bedoya: Tsohon dan kwallon Kolombiya. An haife shi ne a ranar 26 ga watan Nuwamba, 1975. Da farko ya fara yin kwallo ne a matsayin mai tsaron baya (Defender), amma daga baya ya koma yana yin wasa a tsakiyar fili (Midfielder). Rahotanni sun nuna bai taba fita wata kasa don yin kwallo ba, kenan ya yi wasa ne a gida Kolombiya inda ya buga wa kulob da dama. Ya taba buga wa Kolombiya wasa a matakin manya a tsakanin shekarar 2001 zuwa 2009 inda ya yi wasa har sau 49 kuma ya zura kwallaye 4 a raga. An ce dan kwallo yana da saurin fushi idan yana kwallo, da zarar an yi masa keta nan take yake ramawa da hakan ke sa ake yawan ba shi jan kati.
Yanzu dai dan kwallon ya shiga kundin tarihi inda ya zama na farko a duk fadin duniya a matsayin wanda ya fi samun jan kati a kwallon kafa. Rahoton ya nuna yanzu haka ya samu jan katin da suka kai 46.
Haka kuma bayan ya daina wasan kwallon kafa ya zama Mataimakin Koci a wani kulob da ke Kolombiya inda a can ma rahotanni sun nuna alkalin wasa ya ba shi jan kati saboda saboda rashin hakuri.
2. Cyril Rool. An haifi Cyril Rool ne a wani gari da ake kira Pertuis da ke kasar Faransa a ranar 15 ga watan Afrilun 1975. Shi ne na biyu a matsayin dan kwallon da ya fi samun jan kati a tarihin kwallon kafa a duk fadin duniya. Rahotanni sun nuna kafin dan kwallon ya yi ritaya daga buga wasan kwallon kafa ya samu jan kati har sau 27.
Ya buga kwallonsa ne a Faransa a kulob daban-daban. A tsakanin 1993 zuwa 1998 ya buga wa kulob din SC Bastia sannan a tsakanin 1998 zuwa 2004 ya buga wa kulob din Lens. Kulob din sa na karshe kafin ya yi ritaya daga buga wasan kwallon kafa shi ne Marseille inda ya yi musu wasa a 2010.
3. Sergio Ramos: Cikakken sunansa shi ne Sergio Ramos Garcia. An haife shi ne a wani gari da ake kira Camas a kasar Sifen a ranar 30 ga watan Maris, 1986 inda yanzu haka yake da shekara 32. Ramos yana daga cikin ’yan kwallon da yanzu haka suke bugawa kulob din Real Madrid na Sifen. Hasalima shi ne kyaftin din kulob din saboda dadewarsa don yanzu haka ya shafe kimanin shekara 13 yana yi wa kulob din wasa.
Ya fara yin kwallo ne a kulob din matasa na Sebilla da ke Sifen a tsakanin 1996 zuwa 2003 daga nan sai ya koma kulob din manya na Sebilla a tsakanin 2004 zuwa 2005. A 2005 ce ya koma kulob din Real Madrid da ke Sifen kuma har yanzu a can yake buga kwallo.
Tarihin kwallonsa ya nuna ya yi wa Sifen kwallo a matakai daban-daban. A 2002 ya buga wa Sifen kwallo a matakin ’yan kasa da shekara 17 sannan a 2003 ya buga wa kulob din ’yan kasa da shekara 19 (U-19) yayin da a 2004 ya koma kulob din Sifen na manya har zuwa yau.
Sai dai ya kasance dan kwallo na uku wanda ya fi samun jan kati a tarihin kwallon kafa, inda kawo yanzu ya samu jan kati har sau 24 kuma ya kasance na uku a jerin wadanda suka fi samun jan kati a fagen kwallon kafa.
4. Aledis Ruano Delgade: An haifi wannan dan kwallo ne a Malaga da ke kasar Sifen a ranar 4 ga watan Agustan 1985 inda yanzu haka yake da shekara 33. Dan kwallo ne da ke wasa a baya (defender). Ya bugawa kulob da dama a ciki da wajen Sifen kamar haka: A tsakanin 2002 zuwa 2004 ya buga wa kulob din Malaga na Sifen. A tsakanin 2004 zuwa 2006 sai ya koma kulob din Getafe na Sifen. Sannan a tsakanin 2007 zuwa 2010 ya yi wa kulob din Balencia na Sifen wasa. A tsakanin 2010 zuwa 2013 sai ya koma kulob din Sebilla na Sifen. A shekarar 2016 ce ya koma kulob din Besiktas da ke Turkiyya daga nan sai ya koma kulob din Albes da ke Sifen a tsakanin 2016 zuwa 2018. A wannan shekarar ce (2018) ya canza sheka zuwa kulob din Al-Ahli na Masar inda yanzu haka yake buga musu kwallo.
Sannan ya yi wa Sifen kwallo a matakai daban-daban na matasa irin su (U-17) da (U-19) da kuma (U-20) amma bai taba buga wa kulob din manya na Sifen wasa ba.
Yanzu haka shi ne na hudu a matsayin ’yan kwallon da suka fi karbar jan (kati) inda yake da 22.
5. Ronaldo Paolo Montero Iglesias: Shi ne na biyar a jerin ’yan kwallon da suka fi samun jan kati a lokacin da suke yin kwallon kafa. An haife shi ne a ranar 3 ga watan Satumba 1971 inda yanzu haka yake da shekara 47. An haife shi ne a garin Montobideo na kasar Uruguay.
Tsohon dan kwallon da yanzu haka shi ne Manajan kulob din Rosario Central da ke Uruguay, ya samu jan kati har sau 21.
Ya buga wa kulob da dama a ciki da wajen Uruguay. A tsakanin 1996 zuwa 2005 ne ya buga wa kulob din Jubentus na Italiya.
A 2014 ya fara horar da kulob din Penarol, yayin da a 2016 ya koma horar da kulob din Boca Unidos amma bai dade ba ya sake komawa kulob din Colon de Santa Fe duk a 2016. A bara (2017) ne ya koma horar da kulob din Rosario Central, kulob din da yake horarwa har yanzu. Dukkan wadannan kulob suna zaune ne a kasar Uruguay.
A tsakanin 1991 zuwa 2005 ya buga wa kungiyar kwallon kafa ta Uruguay kwallo. Ya yi wasa har sau 61 kuma ya samu nasarar zura kwallaye 5 a raga.
6. Paolo Alfaro Armengot: Shi ne cikakken sunansa. An haife shi ne a ranar 26 ga watan Afrilu, 1969 inda yanzu haka yake da shekara 49. Dan kwallo ne da ya yi wasa a tsakiyar baya (Central Defender). Sannan shi ne na shida a jerin ’yan kwallon da suka fi samun jan kati a tarihin kwallon kafa a duniya, inda ya samu jan kati a lokuta daban daban har sau 18.
An haife shi ne a garin Zaragoza na kasar Sifen. Kafin ya daina kwallo, ya buga wa kulob da dama wasa da suka hada da Real Zaragoza a tsakanin shekarar 1989 zuwa 1992 sai FC Barcelona a tsakanin shekarar 1992 zuwa 1993 sai Racing Santander a tsakanin 1993 zuwa 1996.
Sauran kungiyoyin da ya yi wa wasa sun hada da Atletico Madrid a tsakanin 1996 zuwa 1997 sai Merida a tsakanin 1997 zuwa 2000, sai Sebilla a tsakanin 2000 zuwa 2005 sai ya sake komawa Racing Santander a tsakanin 2006 zuwa 2007, daga nan ne ya yi ritaya daga buga kwallon kafa.
Sai dai ya fara horarwa ne a shekarar 2009 inda ya horar da kulob da dama a Sifen da suka hada da Leganes da Huesca da Manbella da kuma Mirandes. Kulob din da ya horar na karshe shi ne Mirandes a tsakanin 2017 zuwa 2018.
7. Yannick Cahuzac: Shi ne na bakwai a jerin ’yan kwallon da suka fi samun yawan jan kati a rayuwarsu ta kwallo. An haife shi ne a garin Ajaccio na kasar Faransa a ranar 18 ga watan Janairun 1985 inda yanzu haka yake da shekara 33.
Ya samu jan kati har sau 17 da hakan ta sa ya zama na 7 a jerin ’yan kwallon da suka fi samun jan kati a fagen kwallon kafa.
Tarihi ya nuna ya buga wa kulob biyu ne kacal a kasar Faransa. A tsakanin shekarar 2005 zuwa 2017 ne ya buga wa kulob din Bastia wato ya shafe kimanin shekaru 12 yana yi musu kwallo kafin ya canza sheka a 2017 inda ya koma kulob din Tolouse, kulob din da yake yi wa wasa har yanzu. Tarihi ya nuna bai taba bugawa kasar haihuwarsa Faransa kwallo a matakin manya ba. Yana wasa ne a tsakiyar fili amma mai lura da baya (Defensibe Midfielder).
8.Cikakken Sunansa shi ne Felipe Melo de Carbalho. An haife shi ne a ranar 26 ga watan Yunin 1983 inda yanzu haka yake da shekara 35. An haife shi ne a wani gari da ake kira Bolta Redonda da ke Brazil. Yana buga kwallo ne a tsakiyar fili (Midfielder). Dan kwallo ne da ya yi fice a ciki da wajen Brazil a fagen kwallon kafa. Ya buga wa kulob da dama a ciki da wajen Brazil da suka hada da kulob din Flamengo da Cruzeiro da Gremio da Internazionale da kuma Palmeras duk a cikin Brazil. Sauran kulob din da ya yi musu kwallo a wajen Brazil sun hada da Mallorca da Racing Santander da Almeria duk a Sifen sannan akwai Jubentus da Fiorentina a Italiya da kuma Galatasaray a Turkiyya.
Yanzu haka yana buga wa kulob din Palmeras kwallo ne a Brazil. Tarihi ya nuna ya samu jan kati har sau 14 a lokuta daban-daban da hakan ta sa ya zama na takwas a jerin ’yan kwallon da suka fi samun jan kati a fagen kwallon kafa.
©aminiyahausa.com
Post a Comment