1. Na farko su fara da gaisuwa irin wadda addinin muslunci ya tanadar mana (watau suyi wa junan su sallama).
2. Sai Ango ya daura hannunsa a bisa goshin Amaryarsa ya karanta wannan addu'ar:
"Allahumma innee as'aluka min khairiha wa khairi maa jabaltaha 'alaihi wa'a uzhubika min sharriha wa sharri maa jabaltaha 'alaihi"
(Abu Dawud Ibn Maajah Al-Haakim Al-Bahaki da Abu Ya'ala).
3. Daga nan sai Ango da Amarya su gabatar da Alwala sannan su gabatar da Sallah raka'a biyu bayan sun idar sai su karanta addu'o'i na neman 'ya'ya na gari.
4. Kafin Ango ya gabatar da jima'i da Amaryarsa anaso ya fara bata maganganu na kwantar da hankali da soyayya sannan yayi wasanni da ita.
5. Idan Amaryar budurwace anaso Ango yayi jima'i da ita sannu a hankali, kada ya matsa sai ya kosar da sha'awarsa a wannan dare.
6. Kada Ango ya tada hankalinsa don baiga bayyanar jini ba bayan saduwa da budurwar Amaryarsa don kuwa akwai dalilai da dama da zasu sa murfin budurci ya fashe kafin ayiwa bidurwa aure, wadannan dalilai sune: Kwararowar jini da karfi a lokacin haila, rashin lafiya, hawan Doki ko keke a lokacin wasanni, faduwa haka kawai in tsautsai ya ratsa.
7. Anso lokacin da Ango ya shiga dakin Amaryarsa ya bata wani abin tabawa (watau abinci).
Post a Comment