Dan wasan Najeriya, Ahmed Musa ya bukaci Hukumar kwallon kafa ta Afrika da ta gudanar da bincike domin tantance sahihancin kwallaye 2 da Super Eagels ta Najeriya ta jefa a ragar Afrika ta Kudu amma alkalin wasa ya soke a karawar da suka yi a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika.
Alkalin wasan dan asalin Gambia, Bakary Gassama ya soke kwallayen da Kelechi Iheanacho da Ahmed Musan suka zura a ragar Afrika ta Kudu kuma babu wasu kwararan dalilan da suka saka ya hana kwallayen.
Koda yake alkalin ya amince da tafka kuskure , sannan kuma ya nemi afuwan Musa, in da ya ce, wani lokacin ana samun irin wannan kuskuren musamman saboda rashin na’urar taimaka wa alkalin wasa.
Tuni dai Najeriya ta samu nasarar samun tikitin halartar Gasar Cin Kofin Afrika .wanda za’ayi a kasar Kamaru a shekara mai zuwa duk da cewa ta tashi wasan ne 1-1 da Afrika ta Kudu a birnin Johannesburg.
Najeriya dai kawo yanzu tana matsayi na daya acikin rukunin da maki 11 sai kasar Afirka ta kudun a matsayi na biyu sai kuma kasar Libya a matsayi na uku yayinda kasar Sychelles take a matsayi na hudu kuma na karshe.
Sources:Leadershiphausa.com
Post a Comment