Shugaba Muhammadu Buhari yayi juyayin kisan Sojin Najeriya 118 da 'yan ta'adda suka kashe a Metele - Shugaban kasar ya bayyana cewa zai yi aiki tare da shugabanin hukumomin tsaro da binciken sirri domin daukan mataki
- Shugaba Buhari ya yi kira da 'yan Najeriya su dena jefa siyasa cikin al'amarin kisan sojojin Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana jimaminsa kan kisar da mayakan Boko Haram suka yiwa sojojin Najeriya a kauyen Metele da ke jihar Borno inda ya tabbatar da cewa za a dauki matakan kare afkuwar hakan a gaba. Kalaman na shugaban kasar yana zuwa ne kwanaki shida bayan mummunan harin ta bakin mai magana da yawun shugaban kasar, Garba Shehu.
Mr Shehu ya ce, "Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da mayar da hankali wajen tsare lafiyar jami'an soji da ma sauran al'ummar kasar baki daya. A cewar shugaban kasar, "Babu wani shugaba da zai nade hannu yana kallo 'yan ta'adda suna barazana ga rayyukan jami'an soji da sauran al'umma. Jami'an sojin mu sun nuna bajinta da jarumta a kan yan ta'adan kuma zamu cigaba da basu dukkan gudunmawar da suke bukata domin kawo karshen wannan masifar.
A cikin kwanakin nan, zan cigaba da aiki tare da shugabanin soji da shugabanin hukumomin tara bayyanan sirri domin sannin matakin da za a dauka." "Shugaban kasar ya bayyana cewa yaki da rashawa matsala ce da ta zama ruwan dare a kasashen duniya wadda ke bukatan hadin gwiwa tsakanin kasashen da ke fama da fitinar.
"Shugaba Buhari ya tabbatarwa 'yan Najeriya cewa gwamnatinsa ba zata karaya ba wajen cigaba da yaki da rashawa da dorawa kan nasororin da aka samu a kan yan ta'addan.
"Ya kuma shawarci yan Najeriya su guji jefa siyasa cikin al'amarin inda ya ce dakarun sojin Najeriya sun sadaukar da rayuwarsu ne domin samar da tsaro ga dukkan 'yan Najeriya."
A baya, Legit.ng ta kawo muku cewa a kalla sojoji 118 ne suka rasa rayukkansu sakamakonn harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai a ranar 18 ga watan Nuwamba a sansanin soji da ke Metele a jihar Borno. An kuma tabbatar cewa har yanzu akwai wasu sojoji 153 da ba a gano inda suke ba kimanin mako guda bayan harin da aka kai a sansanin na sojin kamar yadda wasu manyan shugabanin soji suka fadi.
Post a Comment