BA MA SON KUDIN KA: MAGU YA WATSA GANDUJE K'ASA A IDO.
Shugaban hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, Ibrahim Magu ya mayar da hannun Kyauta baya, inda Yaki karbar kyautar Naira miliyan goma da Ganduje ya baiwa hukumar domin shirya gasar gudun yada kanin wani.

Magu ya bayyana cewar hukumar bata karbar tallafi na kudi daga hannun Gwamnoni. A ranar Litinin ne dai mai magana da yawun Gwamnan Kano Aminu Yassar ya bayyana cewar Gwamnan ya baiwa hukumar tallafin Naira miliyan goma dan ta shirya wata gasar tsere.

Sai dai a lokacin da yake mayar da martani kan batun, kakakin hukumar Tony Orilade ya bayyana cewar hukumar ya nesanta kanta daga karbar wadancan kudade da aka ce Ganduje ya bayar.

“Kokarin karya lagon hukumar ne na yaki da cin hanci da rashawa, wani Gwamna ya dauki kudi ya baiwa hukumar “ A cewar Orilade.

MAJIYA: Daily Nigerian Hausa

Post a Comment

 
Top