Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya aikewa majalisar dokoki ta jaha da wasika inda ya gabatar da sunan Hon Manir Dan Iya a matsayin sabon mataimakin Gwamnan jahar Sokoto, kasancewa tsohon mataimakin gwamna Alh Ahmad Aliyu ya sauka daga mukamin nashi da kanshi .Don haka kakakin majalisar Alh Salihu Mai Daji ya bada umurni a aikawa Alh Manir Daniya da wasikar gayyata domin bayyana a zauren majalisar gobe alhamis idan Allah ya kaimu domin tantancewa.

Post a Comment