Taurarin fina-finan Indiya, Deepika Padukone da Ranveer Singh kenan da suka yi aure a kasar Italiya a makon da ya gabata, auren nasu ya dauki hankula a Indiya da ma wajan kasar musamman ga masu sha'awar fina-finan Indiya.
An daura auren nasu ne a kasar Italiya kuma sun yi amfani da abubuwan al'adarsu wajan shagulgulan auren da aka kwashe kwanki biyu ana yi. Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan uwa da wasu zababbun abokan arziki na kusa ne kawai suka halarci auren.
Ya zuwa yanzu dai ma'auratan sun koma kasar su ta Indiya sun kuma nufi garin su amaryar inda ake tsammnin can ma za'a gudanar da shagali na musamman.
Post a Comment