Jaruma Fati Mohammed da Jarumi Aminu Shareef Momo sun Jagoranci tawagar Yan masana'antar shirya fina finan Hausa Kannywood zuwa wajen dan takarar Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar don nuna cikakken goyon baya.
A lokacin ziyarar Jaruman sun bayyanawa Alhaji Atiku Abubakar cewar zasu yi amfani da shafukan su da masoyan su wajen mara mishi baya domin cimma gaci.
A lokacin ziyarar baya ga Fati Mohammed da Aminu Shareef Momo an ga fuskokin Jarumai da dama ciki harda Balarabe Jaji da Zaharaddeen Sani da Nura Zarge da sauran Manyan Jarumai.
Idan baku manta ba mun kawo muku rahotan cewar wasu Jaruman kamar su Sarki Ali Nuhu da Adam Zango da Jamila Nagudu da Fati Washa da sauran Jarumai su kuma sun karkata zuwa ga marawa shugaban kasa Muhammad Buhari baya.
Post a Comment