SHAIKH DAHIR USMAN BAUCHI yana daya daga cikin manyan malaman Darikar Tijjaniya a Nijeriya kuma babban Malami a cikin malaman Afrika ya bayyana dalilai da kuma makasudin da ya sanya suke gudanar da Maulidin Annabi Muhamadu dan Abdullahi, Mahaifin Sayyida Fatima. A wani tattaunawarsa da LEADERSHIP A YAU za ku ji yanda Shehi ya bai wa masu kallon maulidi a matsayin bidi’a shawarar da su daina domin a cewarsa babu makiyin Annabi Muhammadu da zai ga falala a rayuwarsa. Ga dai hirar kamar yanda ya yi da KHALID IDRIS DOYA ya yi da shi a kan maudlin Annabi Tsira. Kasantuwar zagayowar watan da aka haifi Annabi Muhammad, ko Shehi Dahiru Bauchi na da wani abun cewa akan wannan Maulidi? Alhamudullah, da farko ina taya al’umman duniya murnar shigowar watan maulidi, watan murna, watan shigowar alheri, watan da aka haifi fiyayyen halitta, kowa na murna da wannan watan da Annabinmu ya zo a cikinta. Alhadullahi sai mu kara gode wa Allah. Yanda muka ga farkonsa Allah ya sa mu ga karshensa lafiya, Allah kuma ya sa mu samu dacewa da alhairai a cikinsa masu yawa. yanda watan ya saba zuwa mana da alherai ya kwaso mana ya kawo mana muna fatan Allah zan kara mana wannan ni’imar, kuma muna rokon Allah ya sa albarkacin wannan watan ya kawar mana da sharri da bala’o’i.
Takamaime wai mene ne ya sanya kuke wannan maulidin a duk shekara? A dunkule dai maulidi nuna godiya ne ga Allah, da kuma bayyana murnarmu a fili da kuma boye. Allah yana cewa “Ku gode wa ni’imar Allah in da gaske kuke yi ku masu kadaita Allah ne masu bauta masa” kullum ya muku alheri to ku gode masa. Babu wata ni’imar da ta zo duniyar nan da ta kai zuwan Annabi Muhammad (SAW) ‘Wa Ma Arsalnaka Illa Rahmatan Lil’Alamin’.
A bisa haka muke nuna godiyarmu mu gode wa Allah a duk lokacin da watan ya zago. Manzon Allah ya shigo mana duniya ya zo ya yi shekaru 63 wato shekara 21 sau uku ko kuma shekara 7 sau tara. Godiyarmu bata tsaya nan ba, muna kuma gode wa Allah da ya sanya mu daga cikin wadanda suka yi imani da abun da ya zo mana da shi kuma muke bin tafarkinsa har muke raya watan da aka haifesa da murna da kuma nuna soyayyarmu a fili da boye wannan abun godiya ne ga Allah. Kasantuwar akan yi zaga gari har ma a zo a yi ta bukukuwa na raya maulidiji a makarantu da kuma wurare daban-daban, ko akwai wasu abubuwa da aka fi son masu maulidi su maida hankali a kai ko kuma darasin da ake koya a ciki ne? Daman ai irin wannan maulidijoji da kuma zagayen garin ana yinsu ne don nuna murnar, a nuna murnar a fili, amma in aka zauna ba a yi wani abu ba ka ga ai ba’a nuna murnar ba ke nan. Shi ya sa muke nuna murna a ko’ina lungu da sako a yi wa Allah zikiri a kuma yi wa Annabi Salati, a karanta Alkur’aninsa a kuma bayyana wa duniya tarihinsa don al’umma su san kyawawan dabi’unsa su kuma yi koyi da su. A lokacin da ake zaga garin nan ana murna da ranar haihuwar Annabi (S) mutumin da ba musulmi ba, idan ya zo ya tarar da babu wajen wucewa idan ya ce ‘What Happen’? Meye haka, meye ke faru haka ne, sai a ce masa ai ‘Birth Day Celebration’ ne ake yi na Prophet Muhammad (SWA) zai gada kai ya ce au haka, ka ga shi an sanya masa wani karatu a kwakwalwa, zai kama tunanin cewar ashe haka Annabin nan yake a duniya daga nan zai tsunduma neman tarihin wannan Annabin daga nan kuwa in Allah ya sa mai rabo ne sai ka ga ya ribanci wani abu na daga falalar Annabi tun da Manzon Allah rahama ne ga kowa da kowa, Rahamatul Lil-Alamina…..
Ita Maulidin nan ma yanzu har cikin hutun gwamnati aka shigar da ita tsabaragen muhimmancinta, a da can baya ba a sanya ta ba; har hakan ya sanya wasu ke mamaki, wai meye sa ake dakatar da aiki gabaki daya a ranar Maulidin Manzon Allah ne kam? To abun da ya faru ga wanda bai sani ba, bar na fada masa, a cikin alif da 1960 Shehu Ibrahim Kaulaha ya zo Nijeriya ya sadu da Firaminista Abubakar Tafawa Balewa ya ce na zo na maka/ku murna Nijeriya ta samu ‘yancin kai.
Banasare ya ba ku ‘yanci ya bar muku kasarku ta koma hannunku musamman kai da Nnamdi Azikwe kai kana Minista shi kuma yana shugaban kasa, shi kirista ne kai musulmi ne, amma ina da labarin Dakta Azikwe yana zuwa coci ranar lahadi mulki bai hana masa ba, amma kai ma ina tsammanin mulkin ba zai hana maka zuwa juma’a ba ko? Ya ce masa yana zuwa har ma Shehu ya tambaye ‘NI’ yana zuwa sallar juma’a? na ce masa in ya zo Bauchi muna kallonsa yana yi amma a Legos kan ban sani ba; sai ya ce masa kamar yanda kai kake zuwa Massalaci shi kuma yake zuwa Coci ga shi yana ba da hutu a ranar haihuwarAnnabi Isa (a matsayin da shi a daukeshi) wato ranar kirsimeti, sai Shehu mai Kaulaha ya tambayi Tafawa Balewa cewar kai kana ba da hutu ranar haihuwar Annnabinka AnnabiMuhammad (s) sai Firaminista ya amsa da cewa a’a, sai ya ce wa Shehu na ka shaida daga yau na shigar da maulidi Manzon Allah (s) cikin gwamnatin Nijeriya kamar yanda ake shigar da Maulidin Annabi Isa a ciki a ba da hutu na musamman. Daga wannan lokacin ne Maulidin nan ya zama na doka kowace gwamnati ta zo dole ta bi wannan dokar a ba da hutun aiki, tun daga gwamnatin Tarayya, Jahohi da na kananan hukumomi. Da kuma an bar shi ne kawai a hanun malamai, da Islamiyoyi. Shi Shehu ya ce dukkanin Idi na duniya, ba sai wani abu ya faru bane ake Idi? Misali in mako ya cika a ka zo juma’a sai a yi idin juma’a, an ba da umurnin a yi azumi an samu an yi washe gari sai a maida ranar na godiyar Allah, Idin Karamar sallah ke nan ko, haka nan kuma Idin babban Sallah kuma Allah ya kira dukkan jama’a na duniya musulmai kowa da kowa ya zo wajen da aka haifi Annabi Muhammadu, inda kuma aka saukar da Alkr’ani, kowa ya zo shekara ta cika shi ne ma’anar hajji, ziyarar inda aka haifi Manzon Allah shi ne ma’anar hajji da umura. Wannan dalilin ne ya sanya ranar tara ga watan zilhajji (ranar hajji ke nan) washe gari sai kira duk duniya su yi wa bakin Allah yanka, sun sauko daga arfa a yi musu yanka na murna (layya ke nan) wannan ranar ta zama ranar godiya wa Allah. Haka misali idan an haifi yaro akan yi suna a yi murna idan an baiwa mutum mukami ko sarauta yakan yi murna da bikin tunawa da ranar da aka ba shi wannan sarautar.
“To Ni A Duniyar Na Duba Ban Ga Wata Ni’imar Da Ta Kai Zuwan Annabi (s) ba”. A sabili da haka ni a wajena babbar Idi ita ce ranar da aka samu Annabi Muhammad in ji Shehu Ibrahim. A da can baya, mu a nan yankin Barebari sun fi dabba’a abun bikin hawa suke yi duk shekara suna kiransa da suna Morekura, ta nan wajen mu kuma ana yi babban biki Daura da Gumel da sauran wurare haka kadan, daga baya sai ta nan muka fara yin bikin amma muna ce masa sallar kaza, a Kano kuma a ce Takutaha amma duk dai ana nuna murna ne da zagayowar ranar da aka haifi wannan Annabin wanda babu kamarsa. Abun kamar wasa, sai abun ya tambatsa yanzu ko’ina duk shekara sai an gudanar da maulidi a ciki da wajen kasar nan lunguna da sakona. Duk da hakan wasu na ganin maulidin da ake yi a matsayin Bidi’a wanda Manzo bai yi ba, me za ka ce Akramakkalahu? Ta yaya za a ce maulidi bidi’a? maulidi ai ba bidi’a ba ne.
yanzu karamar misali da zan baka dukkanin ‘yan Boko ma’aikatan gwamnati ba suna da ranar birth day dinsu ba? Su ba’a yi musu wa’azi aka ce su daina ba sai a ce a daina na Annabi (s)? a idonmu muna gani idan gwamnati ta bai ma wani babban mukami masoyansa sukan sa rana su je su yi ta taya sa murna, kuma in shekara ta zago su yi biki su sake murna, kamar na ga ana haka a Nijeriya ko? Ko ba’a yi ne kam?.
A lokacin da aka zo yin wannan taron idan masoyansa suna son su yi taron wasu kuma sai su gefe su ce maka kana musulmi ka yarda da wannan abun. Wai da wanda suka shirya maka taron da wanda suka ce kada a yi su waye masoyanka? Kila ma don masu mulki ne basu zuwa su ce musu bidi’a ne, ana ci a sha da su, na Manzon Allah ne bidi’a ke nan. Allah ya sauwake. Shin akwai ranar da ta kai ranar murna kamar ranar da Manzon Allah ya ambata Su Abbakar, Usman, Umar da Aliyu da sauran sahabbai ya ce musu dukkaninku ‘yan Aljannah ne wai shi akwai ranar da ta kai wannan a wajen mutum ya yi murna?
Amma sun yi biki? Don kawai mutum Kalmar bidi’a bata masa wahalar fada ba. Duk wanda ya ce maulidi bidi’a ce mai muni tabbas lamarinsa abun tsoro ne, domin duk wanda ya ce Maulidi haramun ne to ba zai karanta Alkur’ani ba; matukar kuwa zai karanta to ya karanta maulidin Annabi Musa tun daga ranar da aka haifeshi har iya karshen rayuwarshi, da gwagwarmayarsa da dawowarsa daga Madiyana, da fafatawarsa da karbar aiki da gwagwarmayarda Fir’auna da halakar da shi da sabuwar gwamnatin da aka samu bayan halakar da fir’auna duk abun da ya faru har zuwa rasuwarsa har aka gama aka zarce aka yi maganar Karuna duk wannan ba maulidin Annabi Musa aka yi ba? Ka duba suratun Kasasu. Maulidin Annabi Musa, haka shi ma Annabi Isa tun daga kan kakarsa aka kawo maulidinsa da gwagwarmayarsa da bayansa da farko, dukkanin Annabawan nan sai ka karanta tarihinsu, zaka ji a cikin Alku’arni a na cewa karanta mana labarin Annabawa, na Annabi Muhmmadu din ne ba za mu karanta wa duniya ba? Duk wanda ya ce maulidi bidi’a ne ya ji kunya ya ma daina karanta Alku’arni. Da karshe mene ne fatan Shehu Dahiru Bauchi? Fatana dai Allah ya fadakar da mu, ya kuma ganar da mu, tsakanin musulmi da maganarAnnabi mutum ya maida maganar Annabi ta fi maganar kowa, aikin Annabi ya fi masa na kowa, sha’anin Annabi ya fi masa na kowa. Allah fa cewa ya yi “Ya kuma matanAnnabi baku kama da kowa”.
Kamar yanda matansa suka fi kowa babu wani abun da bai kamata na Annabi ya fi komai a wajenka ba. Don haka babu yanda za’a ka soki wani abu na Annabi kuma ka zauna lafiya hakan ba zai iyu ba. Mu dai muna sake godiya da samun wannan Annabin Muhammad dan Abdullahi (s). Allah kuma ya sa a gudanar da zagaye da sauran bukukuwan maulidin a dukkanin fadin kasar nan da ma duniya baki daya. Allah kuma ya sa mu dace da ceton Annabi Muhammadu, ya kara mana soyayya a garesa.
Post a Comment