Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da tallafin Naira Miliyan Goma ga hukumar Yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC a shirin da take na yin wasan gudun yada Kanin wani da hukumomin yaki da cin hanci suka shirya domin taya murna ya Shugaba Buhari kan nasarar da yake samu a Yaki da cin hanci da rashawa.

Ganduje ya bada wannan tallafi ne a lokacin da ya gana da jami’an hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da suka kinshi EFCC da kuma ICPC a masaukin Gwamnan Kano dake babban birnin tarayya Abuja.

MAJIYA: Daily Nigerian Hausa

Post a Comment

 
Top