Shugaba Buhari ya bayyana hake ne a wani taron kaddamar da yakin neman zabensa karo na biyu daya gudana a fadar shugaban kasa kuma ya samu halartar gwamnoni goma sha daya, Sanatoci, manyan jami’an gwamnati da jiga jigan yan siyasa.
A yayin jawabin nasa, Buhari ya dauki alkwarin yin garambawul ga fannin ilimin Najeriya gaba daya, inda yayi alkawarin gayara makarantu guda dubu goma goma a duk shekara, a shekaru hudu masu zuwa zai gyara makarantu dubu arba’in kenan don su zama daidai dana zamani.
Haka zalika Buhari ya yi alkawarin horas da malaman dake koyarwa a wadannan makarantu akan dabarun koyarwa na zamani ta yadda zasu baiwa dalibansu igantaccen ilimi, musamman ilimin kimiyya da fasaha.
Bugu da kari shugaba Buhari ya jaddada manufarsa ta cigaba da yaki da cin hanci da rashawa ganga ganga, inda yace “Mun sani kafin mu samu nasara sai mu nada mutunci, kima da daraja, musamman a tsakanin shuwagabannin Najeriya da talakawanta.
“Rashawa na muguwar barazana ga cigaban Nijeriya, duk da kokarin da muka yin a garkame kofar rashawa a Najeriya, mun sani akwai sauran aiki a gabanmu, a shirye muke mu fadada aikin da muka fara a baya ta yadda zamu ririta arzikin kasa domin amfanin yan kasa gaba daya.” Inji shi.
Bugu da kari Buhari ya bayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu a cikin shekaru uku da rabi da ta kwashe bisa mulki. “A shekaru hudu da suka gabata mun yi ma yan Najeriya alkawarin canji a yadda ake tafiyar da gwamnati, kuma munyi kokari matuka wajen tabbatar da wannan alkawari.”
Post a Comment