Wani ya aiko mani da wannan sakon, kuma ya tayar min da hankali. Yana da kyau wadanda abin ya shafa su bincika👇
BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA MASU GIRMA SHUGABANNIN TSARON KASARMU NIGERIA
(with Datti Assalafiy)
Masu girma shugabannin tsaron Nigeria ina muku fatan alheri da yabo bisa kokarin da kuke wajen inganta tsaron Nigeria, Allah Ya taimakeku Ya baku nasara Amin
Bayan haka a bincikenmu na sirri da muke gudanarwa mun gano wata babbar matsala ta fuskar tsaro da ta taso a wani yanki na Kasar mu Nigeria, wannan yanki yana cikin karamar hukumar Tangaza jihar Sokoto dake iyaka da jamhuriyar Kasar Nijer.
Wato akwai wasu mutane da suka tsallako iyaka daga jamhuriyar Kasar Nijer suka shigo cikin wannan yenki na Tangaza a jihar Sokoto da sunan wai suna da'awah, mutane ne farare kamar buzaye ko larabawa ko kuma fulani, suna dauke da manya manyan bindigogi akan wasu irin babura na shiga daji.
Wadannan mutane tuni sun fara bin rugagen fulani suna karbar zakkar dabbobi da karfin tsiya, kawai sai suje rugar bafulatani su lissafa shanunsa sai su kebe wasu suce wannan hakkin Allah ne, zasu tafi dashi su rabarwa mabukata.
A halin yanzu basu fara kisan kowa ba tukunna duk da suna tafe da manyan bindigogi, amma suna yiwa mutane bulala wai da sunan shari'ar musulunci, idan sukaje kauye suka tarar ana kidan buki ko na gargajiya irin na kauye sai su kama mutane suna musu bulala, kuma suna bibiyan masallatan kauyukan suna tilasta yin muhadara da limammansu har su kuresu dasunan wai basu iya jagoracnin sallah ba.
Sannan kuma yanzu haka suna jan ra'ayin mutanen kauyukan cewa duk wanda keda niyya ta shiga cikinsu ayi aikin Allah to kofa a bude take.
Ga sunayen kauyukan da suka mamaya karkashin karamar hukumar Tangaza kamar haka: Bagida, Tunigara, Bajaga, Bugawa, Mano, Mulawa/Mule da sauran wasu kauyuka
Akwai wani daji da aka barwa makiyaya fulani don kiwon shanu to a nan mutanen suka kafa babban sansaninsu, kamar yadda nace basu fara kashe kowa ba amma suna dauke da makamai, kuma mafi yawancinsu ba 'yan Nigeria bane, sannan basu bayyana cewa suna gudanar da aikinsu karkashin wata kungiya ba, cewa suke su masu aikin Allah ne
Shugabannin tsaron mu don girma Allah ku dauki matakin da ya dace, ina jiye mana tsoron tasirin da ISWAP reshen ISIS tayi a Nigeria, zasu iya shigo mana da salo na yaudara su tara dukiya da mayaka kafin sai su aiwatar da mummunan kudurinsu
Na mu bincike ne, mun isar muku Allah Ya shaida, saura ku dauki matakin da ya dace musamman batun tsaurara tsaro da sa'ido akan iyakokin Nigeria dake makwabta da kasashen Nijer, Chadi da Kamaru
Allah Ka bamu zaman lafiya a kasarmu Nigeria Amin.
Post a Comment