Rotanni daga jihar Borno a Najeriya na cewa mayaka da ake zaton 'yan Boko Haram ne sun sace mutane fiye da hamsin a yankin Gamborou kusa da iyaka da Kamaru.

Maharan sun kewaye mutanen ne lokacin da suka je daji yin itace. Wasu mazauna yankin suna shaida wa BBC cewa mafi yawan mutanen wadanda suka baro garuruwansu ne saboda hare-haren Boko Haram.
Sayar da ita ce ita ce sana'ar da mutanen suka dogara da ita. Mafi yawancinsu mazauna kauyen Bulakesa ne da ke kusa da iyaka da Kamaru.

Kawo yanzu dai ba a san inda aka tafi da mutanen da aka dauke ba. Haka kuma hukumomi ba su yi wani karin bayani kan batun ba kawo yanzu.
Bayanai na cewa tun ranar Asabar aka sace mutanen, amma sai yanzu bayanai suke fitowa saboda rashin wayar sadarwa a yankin.
Bayanai kan sace mutanen sun fito ne a lokacin da 'yan Najeriya ke ci gaba da jimamin kashe sojoji sama da 40 a garin Metele da kungiyar ISWA ta yi.


Sace mutane da yin garkuwa da su na daga hanyoyin da Boko Haram ke bi a kasashen yankin Tafkin Chadi a shekaru tara da aka shafe ana fuskantar matsalar tsaro a yankin.

Hukumomin Najeriya dai na ikirarin cewa sun karya lagon Boko Haram, amma hare-haren da kungiyar ke kai wa musamman a baya-bayan nan suna sa wasu 'yan kasar sanya ayar tambaya kan ikirarin.

Post a Comment

 
Top