Wani bankin kananan masana'antu watau Microfinance Bank a turance dake a kan titin Bassey Duke, garin Kalaba na jihar Kuros Ribas ya gamu da babban cikasa biyo bayan wasu barayin da suka dirar masa tare da sace makudan kudaden kwastomomi.

Kamar yadda muka samu, barayin kusan su biyar ne suka kai harin a bankin bayan sun ajiye motocin su a waje da kusan karfe 3 na ranar Alhamis din da ta gabata kafin daga bisani su kusa kansu cikin bankin da tsiya.

Legit.ng Hausa ta samu haka zalika cewa shigar barayin cikin bankin ke da wuya sai suka umurci dukkan mutanen dake ciki da su kwanta sannan kuma suka kwashe dukkan kudaden da ke a bakin kanta sukayi tafiyar su.

A wani labarin kuma, Daya daga cikin tsaffin gwamnonin Najeriya daga jihar Enugu Sullivian Chime ya bayyana cewa gyaran Najeriya fa da shugaba Buhari ya fara ba zai yiwu ba cikin dan kankanen lokaci kamar adda jama'a ke tunani.

Tsohon gwamnan dai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake fira da wakilin majiyar mu a gidan sa dake a garin Enugu, babban birnin jihar.

Naijhausa

Post a Comment

 
Top