Idan tayi fushi jawota jikinka ka rarrasheta, mata suna son rarrashi.
Idan kaga tayi shiru tambayeta meye matsalarta cikin murya mai sanyi bawai da fada ba, al'adan mace ne ko anyi mata abu sai tace ba komai saboda ita komai sai tasa shagwaba kuma tana son mai rarrashinta.
Idan tayi kwalliya ka yabawa kwalliyarta, idan tayi girki kaci kana santi koda dadinsa baikai ayi santi ba.
Idan kukayi kwanciyar aure da ita ka nuna mata kololuwar jindadinka da ita, haka kuma da rana ka dauko zance kana zuzuta ta kana yabawa da irin ni'imarta wannan shi zaisa ta kara kaimi wurin kula da kanta.
Kana yabon kyawawan halinta kuma kana tausayawa mata da yimata uzuri idan tayi ba daidai ba.
Duk sanda ka samu lokaci kana shiga kitchen kana tayata ayyukan gida ko ba yawa ne, mata suna son su gansu tareda mazajensu suna tayasu aiki kai koda zuwa kawai kayi ka zauna bakayi komai ba zataji dadi a ranta.
Idan tace zata matsa daga kusa da kai riketa kace baka yarda ba.
Idan kaga tana kuka sa bakinka ka tsotse hawayenta.
Idan kaga tana kishinka kyaleta kar ka kyareta, so kesa ayi kishi wanda baya sonka bazaiyi kishinki ba.
Idan bata da lafiya ka fita damuwa da halin da take ciki.
Idan kayimata laifi ka nuna rashin jin dadinka da hakan kuma ka bata hakuri.
Duk sanda zaka fita ka sumbace ta a goshinta.
Kana kasuwa ko office kirata ta waya kace kana kewarta.
Kada kalmar (ina sonki ta dinga yiwa harshenka nisa)
Maza ku gane wani abu ba ci da sha da sutura ne kawai zakayi ka burge mace ba . Wata zakaga ba abinda ta rasa na nau'in jin dadi amma tana cike da damuwa me yasa? Saboda ta rasa abubuwanda na lissafo a sama. Wallahi akwai wanda sunfi shekara nawa suna samun matsala da iyalinsa sai kaji yana tutiyar bai rageta da ci ko sha ba sutura ma yanayi kawai halinta ne. Ba halinta bane ta rasa muhimman abubuwane a rayuwarta.
Sau da yawa anbar mazan hausawa a baya wurin kula da matansu kuma sune mafi dacewa da su kula da matansu idan mukayi duba da yanda Manzo S.A.W yakeyi da matansa.
Allah yasa mu dace.
Post a Comment