Wani magidanci dan shekara 25 ya fada hannun mahukunta a gundumar Lom Kao a Phtchabun na kasar Thailand ranar Asabar kuma aka tuhume shi da yi wa matarsa gunduwa gunduwa.

Yansanda sun kama wanda ake zargin Changchai Sae Song a kan babur yayin da yake tserewa tazarar kilomita kadan daga garin Wang Ban.
 
Yanuwansa da yansanda sun sami gawar matarsa  Duangjai Charoenraktrakul yar shekara 24 a cikin gidansu, kuma ya yi mata guntu guntu a wani yanayi na kisan rashin imani a kauyen Thap Boek. Gawar tana kallon kasa, an gundule kai, kafafu, aka caka wuka a bayanta har wuri biyu, kuma aka dada caka wuka guda biyu a al'aurarta.
 
Yanuwansa sun ce an daura ma Changchai aure da Duangjai shekara biyu da suka gabata, kuma suna noman Kabeji ne domin samun madogaran rayuwa, amma Changchai ya zama dan kwaya na gaske, kuma ya shiga tuhumar matarsa kan zamantakewa duk da yaake tana dauke da juana biyu na tsawon watanni shida.

Hakazalika wata majiya ta shaida mana cewa cacan baki ya shiga tsakanin Changchai da matarsa da safiyar Asabar, kuma wani danuwansa ya yi kokarin raba rigimar, amma sai Changchai ya yanke masa yatsa da wuka. Ganin haka ne ya sa danuwansa ya je ya kira yansanda, amma lokacin da suka shigo gidan na katako mai hawa daga, sai suka tarar da mugun aiki da Changchai ya aikata.

DAGA ISYAKU.COM 
 
Copyright, do not copy and paste our news on your blog without express written permission from us
 
Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb
 
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 
 
Domin Flashin ko gyaran wayarka Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

 
Top