SALLAR ASUBAHI sallah ce mai muhimmanci. Allah ya rantse da lokacinta a cikin al-kur'ani.

Allaah yace:-
( والفجر وليال عشر )
Saboda muhimmancin ta ne Allaah ya kirata da sunan "QUR'AANUL FAJR"
Allaah yace:-
( أقم الصلاة لدلوك الشمس إلى غسق الليل وقرآن الفجر إن قرآن الفجر كان مشهوداً )

Dan uwa za ka tauye wa kanka lada mai yawa idan baka tashi ka je ka sallace ta ba.

Za ka rasa darajoji masu dimbin yawa idan ka gagara tashi don sallarta.

Ka tuna fa ita ce Sallar da take yi wa munafukai nauyi

Manzon Allah (SAW) ya ce Nafilar asubahi ta fi duniya da abinda yake cikin ta.
((ركعتا الفجر خير من الدنيا وما فيها))

الله اكــــــــــــــــــبر

Idan har raka'atal Fajri ta fi duniya da abinda yake cikin ta, to ya kake ganin ita kanta Sallar Asubahin?

KANA SON A DASA MAKA BISHIYA A ALJANNA?

Manzon Allah (SAW) ya ce: "Duk wanda ya ce 'Subhanallah, Walhamdulillah, Wala'ilaha Illallah, Wallahu Akbar', za'a dasa masa bishiya a Aljanna da kowanne daya daga cikin su".

Silsilatul Ahaadiisus Sahiha 2880.

Me kake tsammani bayan ka idar da Sallah ka zauna ka yi ta wadannan zikirorin?

Me kake zaton ma'anar za'a dasa maka bishiya a Aljanna? Idan bishiyar taka ce Aljannar da bishiyar ke ciki fa? Tabbas taka ce.

Ya Rabbana duk wanda ya tura wannan har wasu suka karanta suka amfana, Ya Allah Ka dasa masa bishiyoyi a Aljanna iya adadin mutanen da suka karanta suka amfana a dalilinsa.

Post a Comment

 
Top