An kammala zaman tattaunawa tsakanin gwamnonin Najeriya da shugaban kasa Muhammadu Buhari daya gudana a fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa dake babban birnin tarayya Abuja, inda aka tattauna batun karancin albashi.
Majiyar Legit.com ta ruwaito gwamnonin da suka gana da Buhari a madadin kungiyar gwamnonin Najeriya sun hada da gwamnan jahar Legas, Akinwumi Ambode, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu, Akitu Bagudu na Kebbi da Abdul Aziz Yari na Zamfara.
Sai dai gwamnonin sun yi tsit da bakunansu bayan fitowa daga zaman tattaunawa, duk da cewa sun shafe sama da awa daya suna tattaunawar da shugaba Muhammau Buhari a ofishinsa.
A satin daya gabata ne kungiyar gwamnonin Najeriya ta nada wasu gwamnoni biyar da zasu tattauna da Buhari game da batun karin karancin albashi inda kungiyar kwadago ta Najeriya ta nemi gwamnati ta biyasu naira dubu Talatin a matsayin karancin albashi.
Wannan magana ta sanya shugaba Buhari kafa wata kwamiti mai kafafuwa uku wanda ta kunshi wakilan kungiyar kwadago, wakilan bangaren yan kasuwa da kuma wakilan gwamnati, inda aka tattauna kan batun karin albashin a karkashin jagorancin tsohuwar Minista Amal Pepple.
Bayan doguwar tattaunawa, kwamitin ta yanke shawarar gwamnati ta biya karancin albashin naira dubu Talatin, inda a satin daya gabata kwamitin ta mika ma shugaba Buhari rahotonta, inda ta yi kira gareshi daya duba yiwuwar biyan hakan.
Sai dai jim kadan da bayyanar wannan rahoto, sai gwamnoni suka fara korafin cewa basu yarda ba, ba zasu iya biyan naira dubu Talatin a matsayin karancin albashi ba, domin kuwa jahar Legas ce kadai za ta iya biyan wannan albashi ba tare da wata matsala ba, idan kuwa sai sun biya, toh sai sun rage yawan ma’aikata ko kuma gwamnati ta kara musu kudaden da take raba musu a duk karshen wata.
Post a Comment