Sashen jakar magori na isyaku.com a yau dai ya samo wani labari maras dadi, domin dai labari ne ya samo daga garin Ikare-Akoko da ke cikin karamar hukumar Akoko na yamma a jihar Ondo, inda aka kashe wata tsohuwa yar shekara 70 mai suna Madam Medinatu Ala a wani kisa na rashin imani, aka yanke nononta guda biyu da al'aurarta, daga bisani kuma aka cire hanjin cikinta aka tafi da su.

Rahotanni sun ce wannan tsohuwa tana zaune a wani gida mai lamba B/97 rukunin gidaje na Okegbe a Ikare-Akoko.

Saidai wani rahoto ya ce yansanda sun kama wani mutum da suke zargi yana da hannu wajen aikata wannan danyen aiki, kuma yansandan na ci gaba da bincike.

DAGA ISYAKU.COM 

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Domin Flashin ko gyaran wayarka Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

 
Top