Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana gwamnatin shugaba Buhari a matsayin mafi muni da aka taba samu tun dawowar mulkin dimokradiyya a shekarar 1999.


Atiku ya bayyana hakane a lokacin da ya kaiwa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmad Muhammad Makarfi ziyara, Atiku ya kara da cewa, zaka iya shaida cewa tun bayan dawowar dimokradiyya wannan ne yanayi mafi muni da muke ciki ta bangaren tattalin arziki, hadin kan kasa da tsaro.

Ya kara da cewa, akwai kuma rashin sanin makamar aiki da rashin aikin yi da ya karu da tsadar kayan masarufi ga canji kudin kasashen waje yayi tashi gwauron zabi da ya hana masu zuba jari shigowa kasarnan, Atiku yace an bayyana Najeriya a matsayin cibiyar talauci ta Duniya duk da albarkatun kasa da al'umma da muke da ita amma rashin shugabanci na gari ya jefamu wanna hali.

Dan haka yace dole ne a dukufa dan ganin an canja wannan shugabanci, kamar yanda jaridar Cable ta ruwaito.

Ku Ajeyi mana ra'ayoyinku ta hanyar Comments

Post a Comment

 
Top