Sarkin Musulmi kuma Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya karfi bakuncin shugabannin kungiyar Katolika na Najeriya a fadarsa.

Sultan ya bukaci dukkanin shugabannin addini da su hada kai sannan suyi wa’azi akan rikici kafin, lokaci da kuma bayan zabe.

Yace: “Ya zama dole mu fadama kanmu gaskiya sannan mu fadi gaskiya. Abubawa basu daidaita ba a Najeriya. Mu daina fakewa a karkashin addini, kabilanci ko yanki. Na san cewa muna da matsaloli a Najeriya. Kada mu yaudari kawunanmu.


Ya kara da cewa: “Babu fada tsakanin addinin kirista da na Islama. Sai dai kila sabanin ra’ayi tsakanin Musulmi da dan kirista. Amma ya zama dole muyi kokari sannan mu gano yan akika a tsakaninmu. Koda dai mutun ba zai iya gama gane bara gurbin kwai ba daga jama’a. Amma mu cigaba da taka rawarmu don tabbatar da zaman lafiya a kasarmu.”


Basaraken yayi Magana akan hadin kai inda ya kalubalanci yan Najeriya da su daina fakewa da addini, sannan ya kalubalanci shugabanni da su wayarwa da mutane kai cewa Allah daya muke bautawa amma kowa ya zabi sigar yin bautarsa.
Ya kuma yi Magana akan kashe bayin Allah da sunan addini, cewa babu yadda zaka kashe rai sannan kace yana yiwa Allah yaki ne kawai dai kana yaudarar kanka ne.
Read more at: https://ift.tt/2wMX8h0

Post a Comment

 
Top